Da Guba Ciki: Wanda Ya Ci Abincin CORONA A Kaduna Ya Shirya Mutuwa – NAFDAC

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, ta Kasa reshen jihar Kaduna ta gargadi barayin da suka fasa dakin adana abincin agaji na Kaduna da kada su kuskura su ci wannan abinci domin akwai guba magunguna da aka saka a ciki sannan wasu ma sun gurbata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin Gida, na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya saka wa hannu.

Aruwan yace hukumar ta sanar wa gwamnatin jihar cewa an saka magunguna a ciki sannan wasu daga ciki sun lalace da yasa ba za ayi amfani da su ba.

Ya umarci mutanen da suka saci abincin kada su ci, domin kuwa duk wanda ya ci ya kuka da kansa idan wani abu ya same na rashin lafiya.

Sannan kuma gwamnati ta ce zata bi gida-gida don farautar wadanda suka sace wadannan kaya domin kama su da hukunta su.

Idan ba a manta ‘Yan iska a Kaduna sun ja zugar batagari da wasu ƴan unguwa zuwa dakin da ake ajiye abinci dake unguwar Gwari Avenue, dake Barnawa Kaduna, suka rika jidar abinci, a motoci, babura da dakon su a ka zuwa gidajen su ranar Asabar.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe ta ziyarci unguwar ranar Lahadi tare da Kwamishina Aruwan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply