Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar akalla mutum 7 ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Karfi dake karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun yi garkuwa da dagacen kauyen sannan wasu mutum uku sun ji rauni a dalilin harin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta fara farautan wa?annan ?an bindiga.
A ranar Laraba wani dan jarida a kauyen Sale Hussaini ya ce mahara dauke da muggan makamai sun afka kauyen da misalin karfe 11 daren Asabar inda suka zarce kai tsaye zuwa gidan dagace Abdul-Hayatu Ilu suka waske da shi.
Hussain ya ce daya daga cikin mutum bakwai din da maharan suka kashe makwabcin Abdul-Hayatu Ilu ne kuma maharan sun kashe shi ne saboda ihun rika yi a lokacin da aya gansu.