Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun kashe Sagir Hamidu, tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a shekarar 2019, a babban hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Marigayi dan siyasan ya nemi kujerar gwamnan ne a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin kasa.
Maharan sun bindige shi har lahira ne yayin da suka bude wuta kan matafiya a kusa da Rijana misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
Majiya daga jami’an tsaro da suka nemi a boye sunansu sun tabbatar wa da mutuwarsa suna mai cewa, yana daga cikin wadanda suka mutu sakamakon harbin da yan bindigan suka yi.’
Majiyoyi sun ce an bindige fasinjoji da dama da suke nemi su tsere, yayin da wadanda suka bada hadin kai su kuma an tisa keyarwasu zuwa cikin daji.
Wani da ya tsira daga harin kuma ya nemi a boye sunansa ya shaidawa wakilinmu cewa harin ya faru ne a kusa da Rijana. Ya ce: “Masu garkuwar sun yi amfani da rashin kyawun hanyar, wanda hakan ya tilastawa motocci tafiya a hankali kuma a hannu guda a titin.”
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai amsa kirar da aka masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.