Da Dumi-Dumi: Sarkin Jama’are Ya Rasu


Da safiyar yau ne aka sanar da cewa Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jama’are da ke jihar Bauchi, Alhaji Ahmadu Muhammadu Wabi III rasuwa.

Dan marigayin, Alhaji Hassan Samir Ahmad Wabi (Chigarin Jama’are) shi ne ya tabbatar da labarin rasuwar Sarkin ga LEADERSHIP Hausa.

Ahmadu Wabi ya rasu a ranar Lahadi wajajen karfe 12:02 na dare kamar yadda Chigarin Jama’are ya nakalto.

Sarki Ahmadu yana daga cikin manyan sarakunan jihar Bauchi kuma ya jima a kan karagar mulki inda ya shafe tsawon shekaru 51 yana matsayin Sarkin Jama’are.

Sanarwar ta Chigarin Jama’are na cewa: “Innalillahi Wa Inna’ilaihi Raji’un… ALLAH Mai kowa Mai komai Ya dauki ran Abba mun. Mai Martaba Sarkin Jama’are Alh. Ahmadu Muhammadu Wabi III. Yanzu 12:02Am 06-O2-2022. Allah Madaukakin Sarki Ya sa tafi a sa’a. Ya kuma sa Aljannatul Firdausi ta zamto makoma gareshi. In ta mu ta zo Ya sa mu cika da Imani.”

Bayanai daga masarautar Jama’are din na nuni da cewa za a yi wa marigayin Sarkin Small jana’iza da karfe 3:00pm a fadar Sarkin Jama’are.

Related posts

Leave a Comment