Da Dumi-Dumi: Magajin Garin Sokoto Ya Kwanta Dama

Rahotannin dake shigo mana yanzu haka daga birnin Sokoto na bayyana cewa Allah Ya yi wa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Marafa Danbaba rasuwa yau Asabar a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.

Wani babban aminin marigayin ne ya tabbatar da rasuwar Magajin Garin na Sokoto a wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi dashi.

Ana sa ran za a yi janai’zar Marigayin anjima a babban Masallacin juma’a na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake birnin Sokoto.

Marigayin ya kasance ?a ga Aishatu Ahmadu Bello, wadda ita ce babbar ?iyar marigayi Sardaunan Sokoto Marigayi Alhaji Ahmadu Bello.

Magajin Gari Alhaji Hassan Marafa shine Magajin Garin Sokoto na 13 kuma an na?a shi ne a ranar 31 ga watan Oktoban 1997.

Related posts

Leave a Comment