labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana jagorantar wani gagarumin taro na wasu manyan ‘yan siyasa karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.
Fitattun mutane da ?an siyasa da suka halarci taron sun ha?a da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.
Ana gudanar da taro ne a International Conference Centre da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
A jawabin Kwankwaso, ya ce wasu ?an Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar a ?asar suka ha?a kai don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce yun?uri ne na ?an Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.
A cewar Kwankwaso za su du?ufa wajen farfa?o da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ?an kasa a birni da karkara
Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
Kwankwaso ya ce za su yi wa makiyaya gata na ganin cewa ba a cinye musu burtalai ba, sannan za su bai wa manoma dukkan kariyar da suke bukata.
Tsohon gwamnan na jihar Kano, wanda dan jam’iyyar PDP ne, bai bayyana mukamin da yake son nema ba a wannan sabuwar kungiya ta siyasa.
Sai dai ana rade radin cewa zai fita daga jam’iyyar PDP sakamakon rashin jin dadin abubuwan da ke faruwa a cikinta. Kodayake bai tabbatar da hakan ba.