Daga Comr Abba Sani Pantami
Kungiyar malaman Jami’o’i ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi, duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, amma wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
Da yake zantawa da wakilin jaridar Punch wata majiya mai cikakken bayani a cikin hukumar ta NEC ta ce, “Eh, an dakatar da shi”.
Da aka nemi karin bayani, majiyar ta ce, “Shugaban zai fitar da wata sanarwa a hukumance da wannan safiyar ta jumma’a”.