Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Saki Zakzaky Da Matarshi

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sallami Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

Wakilinmu a Kaduna ya ce jim kaɗan bayan bayar da hukuncin ne aka fita da malamin a mota zuwa gida, inda ba su saurari ko ‘yan jarida ba.

“Kotun ta sallame su ne saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja,” a cewarsa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply