Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Abba Mayar Da Sanusi Sarautar Kano

IMG 20240524 WA0093

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa da alama dai Muhammadu Sanusi II ba zai shiga gidan sarauta yanzu ba yayin da babbar kotun tarayya ta dakatar da gwamnatin Kano daga nada sabon sarki.

Kotun Mai shari’a Liman ta bayar da umurnin hana gwamnatin jihar Kano mayar da Sarki Muhammadu Sunusi karagar mulki.

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa alkalin ya bada umarnin ne a daren ranar Alhamis duk da cewa a halin yanzu yana kasar Amurka.

Wani mai rike da sarautar gargajiya, Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba-Dan’Agundi ne ya shigar da kara gaban kotun ta dakatar da nadin sabon sarkin.

Wadanda ake kara a cikin shari’ar sun hada da: gwamnatin jihar Kano, majalisar dokoki, shugaban majalisar, da babban lauyan gwamnatin Kano. Sauran sun hada da: Kwamishinan ‘yan sanda, Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), jami’an tsaro na NSCDC da SSS na jihar.

Kotun ta umurci wadanda ake karar da su dakata da aiwatar da dokar rusa sarakunan har zuwa lokacin da za a kammal sauraron shari’ar.

Kotun za ta fara yin zama domin sauraron bangarorin da shari’ar ta shafa kan tauye hakki a ranar 3 ga watan Yuni, 2024.

Labarai Makamanta

Leave a Reply