Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida Ya Cigaba Da Rusau A Kano

IMG 20240229 WA0298

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa wasu mazauna garin Gurin Gawa da ke karamar hukumar Kumbotso sun rasa matsuguni yayin da motar rusau ta gwamnatin Kano ta dira kan gidajensu.

A ranar Lahadi ne hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta rusa gidaje da dama a garin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Wannan rusau dai na zuwa ne duk da umarnin babbar kotun jihar Kano, wadda ta dakatar KNUPDA daga rusa gine-ginen al’umma a yankin.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin, lauyan da ke kare masu kara 23 a rikicin, Abubakar Alhaji Rabi’u Doka, ya ce wadanda yake karewa sun samu umarni daga babbar kotun jihar. Sai dai a cewarsa duk da wannan umarni na kotu, gwamnati karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi fatali da shi, ta aikata abin da ta yi niyya.

“Waɗanda nake karewa sun samu umarni daga babbar kotun jiha kuma mai shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud ce ta jagorancin shari’ar. Kotun ta umurci KNUPDA ta dakatar da rusau.” “Sai dai kuma abin ban mamakin shi ne KNUPDA ta yi watsi da umarnin kotu, ta ci gaba da rusa gine-ginen.

“Domin ɗaukar mataki, masu shigar da kara suna shirin fara tuhumar raini, suna ganin cewa kin bin umurnin kotu da KNUPDA ta yi ya janyo musu hasara mai yawa.”

Lauyan ya ƙara da cewa waɗanda yake wa aiki sun mallaki filaye kusan 32 da rusau ta shafa kuma suna da niyyar neman diyya ta hanyar doka.

Manajan darakta na KNUPDA, Ibrahim Yakubu Adamu, bai amsa kira ko sakon tes da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto a jiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply