Da Ɗumi-Ɗumi: Za A Yi Muƙabala Tsakanin Abdul-Jabbar Da Malaman Kano

Gwamnatin Kano ta amince da shirya mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da sauran Manyan Malaman Jihar Kano da suka fito daga bangarorin addini daban daban.

Cikin sanarwar da Sakataren yada labaran Gwamna Malam Abba Anwar ya fitar, yace nan bada jimawa za a sanar da lokaci da wurin da za a gabatar. Sannan za a jona Mukabalar a daukacin kafafen yada Labarai kai tsaye.

Ana ganin wannan mataki na gwamnatin zai kawo karshen tataburzar dake faruwa a jihar dangane da ɓangarorin Malaman Kano da Sheikh Abdul-Jabbar.

Abdul-Jabbar dai yana fuskantar kalubale daga manyan malamai na ciki da wajen Jihar Kano, biyo bayan salon karatun da ya ke yi a massalacin sa, inda ake ganin karantarwar tashi ta yi hannun riga da tsarin Islama.

Labarai Makamanta

Leave a Reply