Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan Bindiga sun saki Dalibai 27 na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna.
Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa manema labarai hakan inda ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen sakin su tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Daliban na daga cikin dalibai 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata. Bayan biyan kudin fansa daga iyaye da shugabannin makarantar, ‘yan bindigan sun saki 10 kawai daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.
Tun da farko wadanda suka sace su sun nemi Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba su kudin fansa har Naira miliyan 500 amma Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da batun tattaunawar, yana mai cewa ‘yan bindiga sun cancanci a kashe su.