Ƴan bindiga sun sace ɗaliban makarantar Horar da Harkokin Noma da Abun da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna.
Har yanzu ba a san adadin daliban da aka sace ba sai dai BBC ta tuntuvbi kwamishinan harkokin tsaro na jihar Samuel Aruwan wanda ya ce yanzu haka yana cikin makarantar kuma suna bincike kan lamarin.
Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.
Wata ɗalibar makarantar ta shaida wa BBC cewa cikin dare maharan suka shiga makarantar.
Ta ce kusan rabin ɗalibai mata aka tafi da su a makarantar kuma ba a tafi da ɗalibi namiji ko ɗaya ba.
Sai dai har yanzu gwamnati ko jami’an tsaro ba su tabbatar da wannan ba.
Wani mazunin unguwar Mando a jihar ta Kaduna ya bayyana cewa kusan karfe 11 da rabi na dare zuwa 12 sun rika jin harbi amma sun yi zaton a Makaratar Horar da Sojoji ta NDA ne ake yi.
“Dama wani lokaci a NDA su kan yi harbi cikin dare tunda makarantar sojoji ce, don haka mun yin tunanin abin da ke faruwa kenan. Sai da ssuba da muka fita sallah en muka samu labarin abin da ya faru,” a cewarsa.
Mutumin ya bayyana cewa kawo yanzu jami’an tsaro na kewaye da makarantar kuma an kwashe ragowar daliban da ba a sace ba an tafi da su makarantar NDA.
Wakilin BBC Yusuf Tijjani da ya je makarantar ya tabbatar da ganin jami’an tsaro a makarantar da iyaye da suka yi dafifi a bakin kofar makarnatar.
Ya ce ana kidayar ɗaliban da suka rage kawo yanzu waɗanda ba a yi awon gaba da su ba.
Ya kuma ce wasu jami’an tsaro sun ga ƙunson harsasai a cikin makarntar kuma suna aikin tantance su.
Ya bayyana mana cewa akwai ɗalibai kusan 300 a makarantar amma har yanzu babu tabbas kan yawan ɗaliban da aka sace.
Yusuf Tijjani ya bayyana cewa cikin kokarin da jami’an tsaro ke yi har da jiragen sojoji suna shawagi a sama.
Unguwar Mando dai ita ce unguwar da tashar jirgin kasa da filin jirgin saman jihar Kaduna suke don haka ba ta rabo da jama’a.