Rahotanni daga N’Djamena babban birnin kasar Chadi na bayyana cewar Shugaban Kasar Idris Deby ya rigamu gidan gaskiya da safiyar wannan rana ta Talata.
Idriss Deby ya rasu ‘yan sa’o’i bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a baya-bayan nan da gagarumin rinjaye.
Rundunar sojin kasar ta Chadi ce ta sanar da mutuwar shugaban, inda ake zullimin ya mutu ne a sanadiyyar raunin da ya samu a “fagen daga” wurin yaki da ‘yan tawayen da ke hankoron kwace iko da gwamnatin kasar.