Da Ɗumi-Ɗumi: Ngozi Ta Zama Shugabar Ƙungiyar Kasuwanci Ta Duniya

Tsohuwar Ministar kuɗin Najeriya, Dr Ngozi Okonjo Iweala ta zama sabuwar Dirakta Janar ta kungiyar kasuwancin duniya.

A cewar majiyoyi daga gamayyar kasashen Turai, ta zama shugabar kungiyar ne bayan nasara kan Yoo Myung-hee, yar kasar Koriya ta kudu, da tazara mai fadin gaske.

Wannan nasara da Dr Iweala ta samu ta kafa tarihi a matsayin Mace ta farko da ta zama shugaba a Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya.

Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada sunan Madam Ngozi Okonja Iweala a matsayin ‘yar takara daga Najeriya, a lokacin da kungiyar kasuwancin ta yanke shawarar ba mace shugabancin Ƙungiyar a karon farko.

Tuni kasashen duniya suka fara taya ƙasar Najeriya murna akan wannan nasara da ta samu, da kuma fatan sabuwar zaɓabbiyar shugabar za ta ba mara ɗa kunya.

Ana sa ran kungiyar WTO ta sanar da nasarar Okonjo-Iweala yau, rahoto daga Thisday.

Labarai Makamanta

Leave a Reply