Da Ɗumi-Ɗumi: Ganduje Ya Amince Da Kisa Ga Wanda Ya Zagi Annabi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya goyi bayan hukuncin kisa,da aka zartarwa Mawakin nan, Wanda aka samu da lefin yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam.

A makwannin baya ne wata Babbabr kotun Shari’a’r Musulunci ta zartar da Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya ga mawakin da ke unguwar Sharifai a jihar Kano, sakamakon samunshi da lefin yin batanci ga fiyayyen Halitta Annabin Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam.

Sakataren yada labaran gwamnan Jihar Abba Anwar shine ya tabbar da haka cikin wata sanarwa da aka fitar da almurun wannan Rana.

Labarai Makamanta

Leave a Reply