Wasu bayanan da muka samu da sanyin safiyar yau talata na nuna cewa akwai yiwuwar gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagoracin Mallam Nasir Elrufa’i zata rarraba masarautar zazzau zuwa gida uku.
Idan ba a manta ba dai Allah yayiwa marigayi sarkin zazzau Dr Shehu Idris rasuwa ranar 20 ga watan satumbar wannan shekara. Kuma yau kusan kwanaki 16 kenan ba tare da an Nada sabon sarki a masarautar zazzau ba Wanda hakan ya janyo cecekuce da suka daga bangarori da dama. Da farko dai masu zaben sarki sun mika sunayen Wanda suka zaba amman gwaman yace bai aminta da sunayen ba sakamakon zargin rashawa da yaiwa zaben katutu.
Bayanan da ke fitowa yanzu wanda har ya zuwa yanzu bamu tabbatar da sahihanci su ba na nuna cewa gwamnatin jihar Kaduna ta kammala shirin raba masarautar zazzau zuwa gida uku kamar haka:
Masarautar Kaduna wacce zata jagoranci masarautun za a kirata da sunar masarautar Turunku. Sai kuma sarkin Ikara da kudan.
Haryanzu muna jiran sanarwa a hukunce daga fadar gwamnatin jihar Kaduna.
Kuna ganin raba masarautar zazzau zuwa gida uku ya dace?