Rahotannin da muke samu a yanzu daga gidan talabijin na TVC na nuni da cewa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Hon Yakubu Dogara ya fice daga PDP ya dawo APC.
Hadimin Shugaban Kasa, Bashir Ahmed ya wallafa hotunan ziyarar da Dogara da Shugaban riko na APC, Mai Mala Buni suka kai wa Shugaba Buhari.
Sai dai bai fayyace a halin yanzu ko tsohon Kakakin Majalisar ya koma jam’iyyar APC ba. Kazalika, shima a bangarensa, Dogara bai sanar da ficewarsa daga PDP ba.