Rahotanni da muke samu daga fadar shugaban kasa ya nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage tafiyarsa zuwa Landan don ganin likita har sai baba-ta-gani.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar yau Juma’a, 25 ga watan Yuni.
Sanarwar ta bayyana cewar “An dage tafiyar duba lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kasar Burtaniya da aka shirya gudanarwa a yau, Juma’a, 25 ga Yuni, 2021.” “Za a sanar da sabuwar ranar da ta dace.”