Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar yau Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.
Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita. A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.
Batun sauya shugabannin tsaro a Najeriya wani lamari ne da aka da?e ana tada jijiyar wuya akai, inda daukacin jama’ar kasar ke ganin sauya shugabannin tsaron shi zai kawo maslaha dangane da ta?ar?arewar tsaro da ta dade tana addabar ?asar.
Mafiyawanci jama’ar Najeriya na ganin kamar sauya shugabannin tsaron zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro, inda wasu suke da ra’ayi sa?anin haka.
Sauyin shugabannin tsaron dai ya fara aiki nan take