Rahotanni daga Babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jami’an tsaro sun yi nasarar kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB ta Tsagerun Inyamurai da ke son ballewa daga kasar.
Ministan Shari’ar kasar kuma Babban Antoni Janar Abubakar Malami ne ya tabbatar da kama Mr Kanu a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Talata.
Malami ya kara da cewa an kama shugaban IPOB ne ranar Lahadi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya kan zarge-zargen da ake yi masa na neman ballewa daga Najeriya.