Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar hana walwala a wasu sassa na jihar na tsawon awanni 24, kuma dokar ta fara aiki nan take.
Wuraren da aka sanya dokar sun ha?a da yankin kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikum, kuma an tura jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda.
Unguwanni kamar Barnawa, Kakuri da Television da Maraban Rido da unguwar Sabon Tasha da Narayi da Unguwar Romi duk suna cikin wurin da dokar ta shafa.
An bai wa jami’an tsaro umarnin damke dukkanin wanda aka kama ya yi kunnen ?ashi da wannan doka ta hanyar karyata, ta hanyar diban kayayyakin jama’a da kokarin haddasa fitina, kuma jami’an tsaro zasu cigaba da sintiri har abin da hali ya yi.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi tir da abubuwan da ake ta ya?awa a kafafen sadarwa na zamani na yunkurin tayar da hankula gami da kwasar kayayyakin jama’a da wasu ke yi. Sannan an bukaci jama’a da zama ‘yan kasa nagari masu martaba doka da oda.
Bayanin hakan na ?auke cikin wata takardar sanarwa da Kwamishinan tsaro na jihar Mista Samuel Aruwan ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.