Da ?umi-?umi: An Sako ?aliban Makarantar Jange?e

Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta tabbatar da sakin ?an matan makarantar Jangebe da ?an fashin daji suka sace.

Gwamnatin ta ce ?an matan su 279 da aka sace sun sha?i iskar ?anci bayan ?o?arin da aka yi na ganin sun ku?uta sannan dukkansu suna cikin ?oshin lafiya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne ?an fashin daji suka kutsa cikin makarantar tare da sace su.

Da sanyin safiyar Talatar nan BBC ta tattauna da gwamna Bello Matawalle na jihar ta Zamfara kuma ga ?arin bayanin da ya yi:

“Alhamdu lillahi, mun ci nasara ga su an sako su dukansu. Dama guda 279. kuma ga shi yanzu suna shigowa, yanzu muke karbar su da ni da mai dakina. G asu suna shiga gidan gwamnati yanzu ga baki ?aya.”

Wane hali ?an matan ke ciki?

Gwamna Mutawalle: Ga su nan lafiyarsu lau. Kun ji maganganinsu, an kara muku su kun ji su suna magana. Saboda haka bukatar mu dama ita ce Allah ya dawo mana da su cikin koshin lafiya, kuma ga su nan sun dawo babu wani abu da ya same su, babu kuma wanda ya halaka cikinsu.

To ko an biya ku?in fansa kafin aka sako su?

Gwamna Mutawalle: Babu abin da aka biya. An yi komai ne bisa tattaunawar da muka yi da wa?anda su ka shiga tsakani aka yi sulhu. Yanzu su ma gasu nana su wajen talatin da wani abu da su ka tafi su ka tadda wadanda su ka sace ‘yan matan, su yi maganganu da su kuma su ka amso mana su.

Madogara: BBC Hausa

Related posts

Leave a Comment