Wata kotu a jihar Kano da ta dakatar da yin mu?abala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da malaman Kano da aka shirya yi.
A ranar Juma’a ne Mai Shari’a Muhammad Jibrin na Kotun Majistire da ke Gidan Murtala, ya yanke hukuncin sakamakon bu?atar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma’aruf Yakasai ya shigar gabanta.
Barista Yakasai dai ya bu?aci a dakatar da gwamnati daga yin mu?abalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatukansa a daukacin kafofin yada labaran jihar.
Sai kuma bukatarsa ta biyu da yake son ya shiga cikin wa?anda gwamnatin Kano take ?ara, sai dai ba a amince da wannan ba har sai an sanar da Abuljabbar da kwamishinan ?an sandan jihar a cewar kotun.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni na kotu, inda Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan ya yabbatar da cewa babu mu?abala a ranar Lahadi mai zuwa.
Lauyan Barista Ma’aruf wato Barista Lukman Auwalu Abdullah ya ce sun ji dadin umarnin kotun.
Ya ?ara da cewa abin da ya sa Barista Ma’aruf ya shiga cikin lamarin shi ne saboda ya tunatar da dukkan ?angarorin cewa bai kamata a yi mu?abala ba, duba da umarnin kotun na farko na haramta wa Abduljabbar karatu.
A ganinsa yin mu?abalar tamkar an bar shi ya yi karatun ne wanda hakan soke umarnin kotun ne da yi mata rashin biyayya.
Yanzu dai an tsayar da ranar 22 ga wata Maris din da muke ciki don sauraran ro?on Barista Ma’aruf Yakasai kan dukkan bu?atun.