Labarin da ke shigo mana a yanzu yanzu na nuna cewa kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta janye daga yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai da safiyar yau Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta biyo bayan ganawar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya tun daren jiya Talata wadda aka shafe tsawon lokaci ana tattaunawa.
Ogunyemi ya kara da cewa mambobin kungiyar ASUU sun janye yajin aikin ne da sharadin gwamnati ta cika alkawuranta. Muddin gwamnati ta saba, a cewarsa, zasu koma yajin aiki ba tare da sanarwa ko talala ba.
Yayinda aka tambayeshi shin an fara biyansu albashinsu da suke bi, ya ce an fara biyansu amma ba’a gama ba. Ya jaddada cewa ba dan rashin albashi suka tafi yajin aiki ba.