Uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Aisha, ta ce bullar annobar cutar Korona ya nuna cewa Allah na fushi da mutanen duniya.
Aisha ta bayyana hakan ne ranar Juma’a a Masallacin kasa dake birnin tarayya Abuja, yayin muhadaran murnan cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci.
Yayinda take kira da a kara kaimi wajen yaki da cutar, ta yi kira ga ‘yan Najeriya su taimakawa kasar da addu’an zaman lafiya da cigaba yayinda ake murnan shekaru 60 da samun yanzin kasar.
“Duniyar nan ta canza sakamakon annobar nan kuma annobar na nuni ga cewa Allah madaukaki yana fushi da mu,”.
“Akwai bukatar mu nemi gafara. Ina tunanin bamu da wata mafita da ya wuce neman gafara daga Allah.”
Uwargidan shugaban kasan ta bukaci ‘yan Najeriya su cigaba da goyon bayan kokarin gwamnatin nan na tabbatar da jin dadin ‘yan Najeriya.
“Shugaban kasa ba zai iya shi kadai ba. Yana bukatan goyon baya da hadin kan dukkan ‘yan Najeriya, da wadanda ya baiwa mukami,” .
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da uwargidar tsohon shugaban kasa, Hajiya Turai Yar’adua; mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamuran mata, Hajo Sani; uwargidar tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Mairo Al-Makura da uwargidar tsohon gwamnan Zamfara, Asmau Yari.