Cushe Cikin Kasafi Bai Saba Doka Ba – Ministan Kasafin Kudi

IMG 20240316 WA0102

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ministan kasafin kudi Alhaji Atiku Abubakar Bagudu yace ko kadan cushen da akayi cikin kasafin kudin Shekarar 2024 bai saɓa doka ba wanda har za a ta tayar da jijiyar wuya akai.

Ministan na martani ne biyo bayan zargin cushe a kasafin kudin Najeriya da Sanata Abdul Ningi ya yi, wanda hakan ya kai ga dakatar da shi a Majalisar na tsawon watanni uku.

A hannu guda ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira da babbar murya cewa cikin gaggawa a gudanar da bincike kan zargin da sanata Abdul ningi ya yi wa ‘yan majalisar Dattawan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply