Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar batun yi wa kasafin kudin 2023 ciko da majalisar dattawan ke tuhumar ma’aikatar kudi na ci gaba tayar da kura.
Kan wannan batun, Ministar jin kai ta aika wa takwararta ta ma’aikatar kudi wata wasika wadda a ciki ta dora alhakin bayyanar wasu naira biliyan 206 cikin kasafin kudin ma’aikatarta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin wadannan ma’aikatun gwamnatin biyu.
A makon jiya, yayin da ministar jin kai ta halarci zaman majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarta, wani batu ya taso da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Wani mamba na kwamitin ayyuka na musamman na majalaisar dattawan, Sanata Elisha Abbo, ya tambayi Minista Sadiya Farouk yadda – kamar yadda ya ce – yadda wasu bakin naira biliyan 206 suka bayyana cikin kasafin kudin ma’aikatar jin kai, wadda ke ?ar?ashin kulawarta.
Rahotanni a jaridu sun ruwaito Minista Sadiya Farouk na dora alhakin bayyanar wadannan biliyoyin nairorin kan ma’aikatar kudi ta kasar.