CORONA: Zan Sake Rufe Kaduna Muddin Jama’a Suka Nuna Halin Awaki – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru Ahmad El-Rufai yace daga gobe, Alhamis duk wanda zai fita daga gidansa dolene ya saka takunkumin rufe baki da hanci.

Yace kotun tafi da gidanka zata dawo a gobe sannan dolene kowa ya saka takunkumin, sannan kada ka sakashi a jaka ko a Aljihu, sai idan an tambayeka ka fiddo, hakanan, kada ya saka ya rufe maka baki bai rufe maka hanci ba ko kuma ya rufe maka hanci be rufe baki ba, gwamnan yace idan aka kama mutum da wannan, to ya karya doka kuma za’a hukuntashi

Ya bayyana hakane a hirar da ake dashi kai tsaye akan yanayin cutar a jihar Kaduna. Yayi gargadin cewa idan mutane suka yi halin Awaki, saboda Akuyace bata jin magana, to za’a sake kulle gari.

Yace amma ba’a fatan a kai ga hakan, yana fatan kowa na jin wannan umarni kuma za’a bi, amma idan aka kiya, za’a kulle garin, wanda bai jin magana sai ya gogawa mutanen gidansa shi kadai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply