Gwamnatin Kaduna ta ce tana duba yiwuwar sake rufe jihar saboda tashin al?aluman mutanen da cutar korona ke kamawa a baya-bayan nan, “saboda mutane ba sa bin doka”.
Yayin zantawa ta musamman da BBC, Gwamna Nasir Elrufa’i ya bayyana fargabar kada ?aruwar annobar ta fi ?arfin asibitocin Kaduna bisa la’akari da ganin yadda ?wayar cutar ke ?ara bazuwa.
Al?aluman da hukumar da?ile cutuka masu ya?uwa ke fitarwa a kullum sun bayyana gano masu cutar korona 54 ranar Juma’ar da ta gabata.
“Ranar Juma’a za ka ga mutane sun yi cunkoso, to, idan muka ce za mu bu?e masallatan khamsus salawat wannan cunkoso za a ci gaba da shi, ba a bin doka, ba a bin tsare-tsare,” in ji gwamna.
A cikin kwana uku na baya-bayan nan ka?ai, cutar korona ta kama mutum 95 a jihar Kaduna, kamar yadda ?ididdigar NCDC ta nuna.
Duk ?a’idojin da muka bayar wa’nda ya kamata a bi, yawancin mutane ba sa bi. Yau in ka bu?e kasuwa, mutum ?aya in yana da wannan ciwo (irin) yadda ake cunkoso, zai iya ba mutane dubbai, cewar Elrufa’i.
Ya ?ara cewa: “Kuma da yake a kasuwa ne, im ma ka same shi, ka ga yana da ciwon, kana neman wa’yanda za ka jawo ka gwada su, ko sun samu ciwon, a kasuwa ina mutum zai san da wa, da wa ya ha?u?”
Haka kuma gwamnan ya koka kan yadda mutane ke ci gaba da rashin mutunta ?a’idojin ba da tazara a wuraren ibada.
A baya dai, gwamnatin Kaduna ta sa dokar kulle fiye da tsawon wata uku kafin bu?e ta kuma yanzu haka jihar ita ce ta takwas a jadawalin jihohin Najeriya masu fama da cutar korona.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta bu?e wasu wuraren ibada da kasuwanni ba kamar a makwabtan jihar, abin da ya sanya mazaunan Kaduna ciki har da ‘yan kasuwa kokawa.
Elrufa’i dai ya ce maimakon ci gaba da bu?ewa ma, ?ila su sake rufe Kaduna, “a ma koma gidan jiya domin mutane ba su bin doka”.