Fadar shugaban kasar Nijeriya ta yi kira ga babbar murya ga alumma su bi doka da sharudan yaki da cutar COVID-19, ta hanyar rufe fuskokinsu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jamaa su rika rufe fuska kamar yadda ya bada umarni, domin su guji halin da zai kai a sake kakaba dokar kulle.
Jawabin shugaban kasar ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu a ranar Lahadi.
Da yake magana ta shafinsa na Twitter, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ta ji mutane na watsi da dokar bada tazara da rufe fuska.
Sai dai a gefe guda jama’a sun soki lamirin Shugaban ?asa Buhari sakamakon yin fatali da dokar CORONA din wanda shi kanshi ya yi, inda aka hango shi a yayin gudanar sabunta rijistar zama ?an jam’iyya a mahaifarsa da ke Daura, inda aka ga shugaban babu takunkumi a fuskarshi.