Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

CORONA: Za A Yi Wa Buhari Da Osinbajo Allurar Rigakafi A Bainar Jama’a

Babban daraktan hukumar kiwon lafiya a matakin farko (NPHC), Faisal Shu’aibu, ya ce za’a fara yi wa shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, allurar riga-kafin cutar COVID-19 kai tsaye ta akwatin talabijin.

Kimanin kwayar maganin riga-kafin cutar ta COVID-19 100,000 ake sa ran shigo da su ?asar nan a ?arshen watan Janairu, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Da ya ke ganawa da kwamiti na musamman kan ya?i da ya?uwar cutar korona a Abuja, Shu’aibu ya ce za’a nuna yin riga-kafin kai tsaye ta kafar talebijin a ?o?arin wayar da kan jama’a domin su rungumi rigakafin.

Ya ?ara da cewa, zakakuran ma’aikatan lafiya za su mayar da hankali wajen kar?ar allurar rigakafin da zarar ta iso ?asar.

“Za mu so ganin manyan shugabanni kamar shugaban ?asa, mataimakinsa, da shugaban ma’aikata su zo su kar?i allurar a bainar jama’a domin tabbatar musu da cewa riga-kafin ba ya cutarwa. Don haka dole mu shiryawa hakan,” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa “Ko da a ?asashen da suka ci gaba, mun ga yadda bayan bawa ma’aikatan lafiya fifiko, shugabanni ma akan fifita su idan ba so ake cutar ta harbesu ba.”

Ya kara bada misalin cewa: “Misali ko a wajen ya?i, idan kana son kashe abokin gaba sai ka nemi muhimman shugabanninsu, da zarar ka gama da su, sauran sojojin ma za su rasa kwarin gwiwa.

Da safiyar ranar Alhamis ne muka rawaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar Dubai.

Ana ganin cewa shine sanannen dan Najeriya na farko da ya karbi allurar rigakafin kwayar cutar korona tun bayan fitowarta.

An ruwaito cewa mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, shine ya bayyana hakan ranar Alhamis.

Exit mobile version