Ministan Sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya bayyana cewa za afara zirga-zirgar jiragen sama na kasa-da-kasa daga ranar 29 ga Agusta, na wannan shekarar ta 2020 da muke ciki.
Sirika ya ce filin jirage saman Abuja da Legas ne za su fara aiki tukunna, domin tabbatar da bin tsari da dokokin kariya daga cutar CORONA.
Wannan sanarwa na kunshe ne a jawabin da Minista Sirika yayi a taron kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Korona a Najeriya, ranar Litinin.
Sai dai tun bayan fitar da wannan sanarwar, jama’a ke ta cece kuce akan lokaci ya yi da za’a buɗe wuraren ibadu domin jama’a su cigaba da bautar Allah kamar yadda aka saba.
Akwai Jihohi da dama da jama’ar su ke fuskantar damuwa dangane da hakan, binciken da muka gudanar ya nuna cewar jihar Kaduna ce ke kan gaba wajen garkame wuraren ibada a kokarin yaki da cutar CORONA.