CORONA: Za A Ɗaure Duk Wanda Ya Karya Doka

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar ta yin ɗaurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona a Najeriya.

Shugaban kasan ya sanya hannun a dokar ne ranar Laraba a babban birnin Tarayya Abuja.

Kamar yadda dokar sashe 34 na sabuwar dokar ta tanada, duk wanda ya saba, za’a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.

Me dokar ta kunsa?

“Dokar ta kunshi ba juna tazara a dukkan taruka, yayinda dukkan wadanda zasu kasance a wajen su sanya takunkumin rufe fuska, su wanke hannayensu, kuma a duba zafin jikinsu kafin su shiga.

Hakazalika dokar ta tanadi kada a samu mutane sama da 50 a waje guda, illa wuraren Ibada.”

A bangare guda, kasar Sin ta fara yiwa al’ummarta gwajin cutar Korona ta hanyar tura auduga cikin dubura, wannan wata hanya ce da masana sukace tafi bada sakamako na kwarai, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Labarai Makamanta

Leave a Reply