Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 242 a fadin Najeriya.
Kwana takwas a jere yanzu jihar Plateau na zarce Legas da Abuja wajen yawan adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Laraba 2 ga Satumba, shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 242 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Plateau-59
Rivers-27
Abia-22
Lagos-20
Oyo-18
Enugu-17
Kaduna-11
Abuja-11
Ogun-10
Ebonyi-4
Osun-4
Ekiti-4
Delta-3
Edo-3
Akwa Ibom-2
Bauchi-1