Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin Mutane Dubu 1,016 da suka kamu da cutar korona a ranar Larabar tsakiyar Mako a Najeriya.
Sabbin alƙaluman da hukumar ta wallafa a shafinta na twitter sun nuna cewa jihar Legas ce ke kan gaba da mutum 434.
Babban birnin tarayya wato Abuja ne ke biye wa Legas da mutum (155), inda jihar Plateau a karon farko ta zama ta uku mai (94).
Jihohin Kaduna (56) da Rivers (56) da Oyo (30) da Nasarawa (27) da Zamfara (25) da kuma Abia (22) na da mutum fiye da 20 da ya kamu da annobar.
Sauran jihohin su ne Enugu (18) da Kano (18) da Bayelsa (15) da Edo (14) da Ogun (11) da Borno (10) da kuma Ebonyi (10).
Jihohin da kuma suke da mutum kasa da 10 da cutar ta bayyana a jikinsu ranar Laraba su ne Jigawa (7) da Anambra (4) da Delta (3) da Niger (3) da kuma Osun (3).
Da wannan adadi, jumillar mutum 86,576 suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 1,278 suka mutu sannan aka sallami 733,22 bayan sun warke.