CORONA Ta Dira Gidan Sakataren Gwamnatin Tarayya

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da matar sa sun killace kan su, bayan an samu wasu daga cikin iyalan sa sun kamu da cutar korona.

Boss Mustapha ne da kan sa ya yi wannan sanarwa, inda ya ce bayan an samu wasu a gidan sa dauke da cutar, an yi masa gwaji shi da matar sa, amma dai ba a same su da cutar ba.

Ni Da Mata Ta Mun Killace Kan Mu:

“Ina sanarwa cewa ni da mata ta duk mun killace kan mu kamar yadda ka’ida ta gindaya. Kuma zan rika gudanar da ayyukan ofis daga gida.

“Wadanda aka samu da cutar babu wata alama mai nuna su na dauke da cutar korona a jikin su. Mu din ma da aka yi wa gwaji, ba a same mu dauke da cutar ba.” Inji Mustapha, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Yaki Da Korona na Najeriya.

Korona ta bulla gidan Sakataren Gwamnatin na Najeriya, kwanaki uku bayan ya zargi masallatai da coci-coci da laifin sakacin sake fantsamar korona a kasar nan.

A ranar Lahadi sama da mutum 400 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya.

Sannan kuma waau yawan mutuwar da ake yi a kasar nan ana dangantawa ne da cutar korona.

Tuni dai aka umarci jama’a kowa ya kara yin kaffa-kaffa daga kamuwa da cutar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply