CORONA: Najeriya Ta Karbi Rigakafi Daga Ƙasar Rasha

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Juma’a ta karbi samfurin rigakafin cutar korona na ƙasar Rasha. Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin ne ya mika wa ministan lafiyar Najeriya, Osagie Ehanire rigakafin yayin ziyarar da ya kai ma’aikatar lafiyar a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Olujimi Oyetomi.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasar sa ta amince da wani rigakafi da ke bayar da kariya daga coronavirus wanda hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, daga baya ta ce za ta yi nazarin ingancin rigakafin.

Ehanire ya ce ” ba tare da ɓata lokaci ba za a mika rigakafin ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, da Cibiyar Binciken Magunguna ta Najeriya da wasu hukumomin don tabbatar da ingancinsa kafin a duba yiwuwar amfani da shi.
A cewar alƙallumar da hukumar daƙile cututtuka masu ƴaduwa ta Najeriya, NCDC ta fitar a daren Alhamis, fiye da mutum 50,000 ne suka kamu da coronavirus. Alƙalluman sun kuma nuna kimanin mutum 1,000 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar ta korona.

Labarai Makamanta