Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yawan wadanda annobar coronavirus ke halakawa gami da masu kamuwa da cutar a duk rana a fadin duniya ya karu zuwa adadin da ba a taba gani ba cikin watanni, tun bayan bullar annobar daga China a watan Disambar bara.
Alkalumman hukumar ta WHO a jiya asabar sun nuna cewar, cikin sa’o’i 24, mutane dubu 259 da 848 suka kamu da cutar ta coronavirus, kaso mafi yawa kuma ya fito ne daga kasashen Amurka, Brazil, India da kuma Afrika ta Kudu.
A juma’ar da ta gabata kuwa, hukumar lafiyar ta ce jumillar mutane dubu 237 da 743 suka kamu da cutar ta COVID-19, yayinda wasu dubu 7 da 360 suka mutu rana guda a sassan duniya, adadi mafi yawa tun bayan 10 ga watan Mayu.
A halin yanzu annobar ta COVID-19 ta lakume rayukan akalla mutane dubu 601 da 822, yayainda wasu sama da miliyan 14 da dubu 300 suka kamu da cutar a tsakanin kasashe akalla 200.
Cutar ta fi barna a Amurka, inda ta lakume rayuka dubu 140 da 120, sai Brazil, inda ta halaka mutane dubu 78 da 772, sai Birtaniya mai mutane dubu 45 da 273, yayinda Mexico ta rasa mutane dubu 38,888.