Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 252 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:30 na daren ranar Talata 24 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 252 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Plateau-50
Enugu-35
Rivers-27
Lagos-26
Abuja-18
Kaduna-18
Ekiti-10
Kano-10
Taraba-9
Anambra-8
Edo-8
Oyo-8
Delta-7
Ogun-6
Abia-5
Bayelsa-5
Ebonyi-1
Osun-1
Gaba daya: 52,800 jimilan wadanda suka kamu 39,964 aka sallama 1,007 sun mutu.