Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 160 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Asabar 11 ga Satumba, shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 160 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Abuja-39
Plateau-39
Lagos-30
Kaduna-23
Katsina-7
Rivers-6
Oyo-6
Yobe-3
Benue-3
Bayelsa-1
Abia-1
Edo-1
Ekiti-1