Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 132 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Litinin 14 ga Satumba, shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 132 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-52
Gombe-27
Plateau-17
Kwara-10
Enugu-9
Ogun-9
Katsina-3
Ekiti-2
Bauchi-1
Osun-1
Rivers-1
Jimillan wadanda suka kamu: 56,388
Jimillan wadanda aka sallama: 44,337
Adadin wadanda suka mutu: 1,083