Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 125 a fadin Najeriya.
Kwana takwas a jere yanzu jihar Plateau na zarce Legas da Abuja wajen yawan adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Alhamis 3 ga Satumba, shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 125 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-42
Abuja-25
Katsina-14
Kaduna-11
Kwara-8
Ondo-7
Delta-4
Anambra-3
Oyo-3
Edo-2
Ogun-2
Osun-2
Cross River-1