CORONA: Mutane 118 Sun Sake Harbuwa A Najeriya – NCDC

Hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC), ta tabbatar da cewa sabbin mutane 118 sun kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba 2020.

Hukumar NCDC a shafinta na Twitter @NCDCgov, a daren ranar Litinin, ta wallafa cewa jimillar mutane 61558 ne suka kamu da cutar, yayin da mutane 56697 suka warke.

Sai dai hukumar ta wallafa cewa, mutane 1125 ne Allah ya karbi rayuwarsu sakamakon yin jinya na wannan cuta.

Ga dai jadawalin jihohin da aka samu bullar cutar a wannan rana:

Lagos-51

Rivers-26

Imo-12

Osun-8

Plateau-6

Abuja-5

Kaduna-4

Ogun-3

Edo-2

Niger-1

Labarai Makamanta

Leave a Reply