Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar COVID-19 ta sake harbin sabbin mutane 103 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Alhamis 8 ga watan Oktoba, shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 103 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-39
Rivers-21
Abuja-19
Oyo-6
Kaduna-4
Bauchi-3
Ogun-3
Imo-2
Kano-2
Benue-1
Edo-1
Nasarawa-1
Plateau-1
Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 59,841, sai kuma mutum 51,551 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1113 suka riga mu gidan gaskiya.