Shugaban majalisar malamai ta kasa na kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga gwamantin tarayya da na jahohi da su bude makarantu don a cigaba da koyo da koyarwa a ciki.
Sheikh Sani Jingir ya kara da cewa ko kasar Sin da Amurka da suke da anmobar sun bude makarantu ana ci gabada koyarwa. Amma a Nijeriya da ba annobar an rufe yara a gida an hana su zuwa makaranta.
Sheikh Sani ya ci gaba da cewa akwai wasu masu mugun nufi ga ‘yan Nijeriya a cikin mukarraban Gwamnatin Buhari. Ya ce an yi kitso da kwarkwarta, inda ya yi kira ga Buhari da ya yi garambawul a Gwamnatinsa ya cire miyagu a cikin ma’aikatu.
Sheikh Jingir ya yi wanan jawabin ne a yayin da yake gabatar da nasihar Juma’a a masallacin Juma’a na ‘yan Taya dake birnin Jos.
A karshe Sheikh Jingir ya yi addu’a ga shugaban ‘kasa Muhmmadu Buhari da Gwabnan jahar Filato Simon Bako Lalong.