Kwamishinan lafiya na jihar Legas, ya ce gwamnati na kashe tsakanin N500,000 zuwa N1 miliyan a kan kowanne mai cutar korona a jihar idan ta tsananta. A yayin zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Abayomi ya ce yawan kudin da ake kashewa majinyatan cutar ya danganta ne da tsananin da cutar ta yi.
Kwamishinan ya ce suna kashe kusan N100,000 ga majinyacin cutar da bata yi wa tsananin kamu ba. “Domin maganin cutar ga wanda bata tsananta ba ko take tsaka-tsakiya a cibiyar killacewa, muna kashe N100,000 a rana daya,” Abayomi yace.
“Wannan kawai zai iya baku damar kintatar yawan kudin da gwamnatin ke kashewa a kan cibiyar killacewa da kuma magani tare da jinya. “Idan kana bukatar kulawa sosai ko halin da majinyaci yake ciki ya tsananta, muna iya kashe N500,000 har zuwa miliyan daya a rana daya, duk hakan ya dogara da yadda cutar ta kama mutum ne.
“Kana bukatar abun taimakawa numfashi wurin jinyar mai cutar, da wankin jini, magunguna.
A gaskiya akwai matukar wahala a ce an gane nawa majinyacin da cutar ta kama sosai ya ci. “Muna dai kokarin ganewa kuma za mu sanar da ku idan muka kammala,”
Abayomi ya ce jihar ta kafa wurin kula da lafiyar wadanda suka warke daga cutar kuma aka sallamesu daga asibiti. Za a ci gaba da kula da su na tsawon watannin shida zuwa shekara daya.
“Mun fara gano cewa akwai wani abu da ake kira da Post COVID-19 syndrome. Bayan sallamar majinyaci, su kan fuskanci rashin kuzari,” yace. “Za ka iya warkewa daga cutar amma bayan makonni kadan sai kwayar cutar ta dawo tana fita daga jikinka. Duk da babu yawa, amma dole garkuwar jikinka ta ci gaba da kokarin ganin bayan kwayar cutar.
“A yayin hakan, su kan yi korafin ciwon kai, rashin kuzari, gajiya da sauran matsaloli,” ya kara da cewa. Ya kara da cewa, bakwai daga cikin dakunan gwaji masu zaman kansu da aka amincewa da su fara aiki a jihar a makon da ya gabata sun yi gwajin samfur 912.
Kamar yadda yace, a mako na biyu da budesu, sun yi gwajin samfur 1,538. Wannan babbar nasara ce kuma abun jin dadi ne. Kamar yadda cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana, jihar Legas ce cibiyar cutar a Najeriya. Akwai mutum 13,806 da suka harbu da cutar yayin da majinyata 1,993 ne suks warke tangaran kuma aka sallamesu.