CORONA: Muna Kashe 400,000 Wurin Jinyar Kowane Majinyaci – El Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na ci gaba da shan caccaka daga bakin ƴan Najeriya, bayan da ya bayyana cewa Jihar Kaduna ta riƙa kashe wa kowane mai cutar Korona naira 400,000 kafin ya warke.

El-Rufai ya yi wanann bayanin ne a taron Majalisar Sarakunan Arewa, da ya gudana a Kaduna, kuma ya watsa bayanin na sa a shafin Twitter.

A wurin taron ya ƙara tabbatar da cewa sai fa a ci gaba da hattara, domin har yanzu cutar Korona na nan, ba a rabu da ita ba.

Ya ce cuta ce mai cin kuɗade, domin Jihar sa Kaduna ta riƙa kashe naira 400,000 a kan duk mai cutar Korona mutum daya kafin ya warke.

Wannan bayani bai yi wa ƴan Najeriya daɗi ba, inda nan da nan su ka bi shi a guje har cikin shafin sa na Twitter su na caccaka da ragargazar sa.

Idan ba a manta ba, kwanan baya Kwamishinan Harkokin Lafiya na Jihar Lagos, ya bayyana cewa Lagos ta riƙa kashe har naira milyan 1 a kan Mai cutar Korona da ya kusa kai gargarar mutuwa. Shi ma ɗin dai ya sha caccaka kamar El-Rufai.

Dukkan su biyu ɗin dai sun ɗanɗana ciwon Korona sun san zafin sa.

Labarai Makamanta