CORONA: Komawa Ga Allah Shine Mafita – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lamarin annobar Corona virus game duniya ce, kawai komawa ga Allah ne mafita daya tilo da ya rage.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne jiya yayin ganawarsa da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso gabas karkashin jagorancin gwamnan Borno, Babagana Zulum a fadarsa dake Aso Villa.

Ya kuma daura laifin rashin samun nasarar yakin ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati sakamakon bulluwar cutar COVID-19.

Yace “mun zama daya da Amurka, wannan wani abu ne mai ban mamaki. Ina ganin kawai mu koma ga Allah”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply