CORONA: Gwamnatin Zata Buɗe Wuraren Ibadu

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ce sun gama nazarin bude guraren ibada a fadin jihar wadanda aka rufe sakamakon cutar corona.

Gwamnan ya ce za a bude guraren ibadar ne a ranar 7/8/2020 domin ci gaba da ibadu kamar yadda aka saba. Sanann ya yabawa shugabannin addinai bisa hadin kai da suka bayar wajen ganin guraren ibadar na garkame.

Sanann kuma Gwamnan ya bayyana cewa dokar hana tarukan jama’a a fadin jihar wacce aka sanya ta saboda bullar cutar cobid-19 za a janye ta daga ranar 20/8/2020.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Legas, Gwamna Sanwo-Olu ya gargadi mutane da su ci gaba da bin matakan likitoci na bada tazara da sanya takunkumin fuska don gudun yada cutar corona da ta ki ci ta ki cinyewa a fadin Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply